Har yanzu gwamnatin Najeriya bata hukunta kowa ba dangane da batan kyautar dabinon Saudiyya.

0 88
Har yanzu gwamnatin Najeriya bata hukunta kowa ba danganta da batan kyautar dabinon Saudiyya.

A Shekarar data gaba ta ne gwamnatin kasar Saudiyya kyautar ton 200 na dabino domin rabawa masu azumi marasa galihu, har iya yanzu gwamnatin Najeriya bata binciko, ko bayyana mutanen dake da hannu cikin wannan makarkashiya ba.

Kasar Saudiyya ta mikawa hukumomin Najeriya dabinon ne domin rabawa mutanen dake zaune a sansanin ‘yan gudun hijira da kuma masallatai. Sai dai wani abin haushi, dabinon ya kare a shagunan ‘yan kasuwa da wurin ‘yan talla a titunan jihohin Najeriya musamman a jihar Abuja da Borno.

Hukumomi basu raba dabinon kamar yadda gwamnatin Saudi ta umarta ba. Dabino na da matukar muhimmanci wajen bude baki ga masu azumi kamar yadda addinin musulunci ya fada a cikin litattafai.

 Gwamnatin Najeriya ta aike da takardar neman afuwar kasar Saudiyya bisa abinda ya faru tare da daukan alkawarin binciko masu hannu cikin wannan badakalar karkatar da dabinon domin hukunta su.

 Karamar ministar harkokin kasar waje, Khadija Abba Ibrahim, ta bayyana cewar ba’a yi amfani da dabinon ta hanyar da ya kamata ba, sannan ta bayar da hakuri a kana bin kunyar da ya faru. Saidai wani rahoto da jaridar Premium Times ta wallafa ya ce ma’aikatar harkokin kasashen waje tayi kunnen uwar shegu bayan tuntubar ta a kan matsayin binciken karkatar da dabinon.

 Kazalika jaridar ta ce ton 200 na dabinon da kasar Saudi ta bayar yana da daraja a kasuwa da ta kai na kimanin miliyan N20m.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.