Harsashen Abinda Zai faru da ‘Yan KannyWood Idan Aka Canza Gomnati

0 234

Alal hakika masu shirya finafinan Hausa sun dade suna tasiri a harkoki daban-daban sannan sun bada gudunmawa wajan isar da sako tare da samarwa kansu sana’ar yin mai makon zaman kashe wando.

Wannan da ma wasu dalilai ya sa ‘yan Fim sun zama sha kallo a tsakanin masoya, sannan sun zama wasu mutane na masumman ga masu kallonsu yau da kulun, haka sun cigaba da jan zaransu yanda suke so.

Sun dade suna haskewa tare da rike kambun farin jininsu a tsakanin masoya, inda ta kai dan fim yana da wata kima ta musamman a wajan jama’a da suka hada da masu mulki da ‘yan siyasa da sarakuna da masu kudi da sauransu.

Sannu a hankali wannan daraja da kimar su tana cigaba da wanzuwa bisa ma’aunin cewa su wasu mutane ne masu fadakawar da wa’azantara wani lokaci ma har da nishadantarwa a cikin wannan al’umma ta mu.

Yana daga cikin dalilin da yasa wasu gungun jama’a masu budurwa zuciya suka rika amfani da wannan damar da suke da ita domin biyan bukatunsu sannan mutanen ko dai suna da kudi ko suna rika da mukami da suke amfani da shi wajan jawo ‘yan fim a jikinsu musamman ‘yan matan su domin cimma wata manufa.

A baya dan fim ko yar fim suna da wahalar gaske su zo waje baka gane cewa wani mutun ya zo ba, amma sannu a hankali wannan kima da daraja ta rika kwaranyewa ta hanyar bata gari daga cikin su kafin daga baya su bata ruwa ba domin su sha ba.

Kamar yadda ‘yan siyasa suke da magoya baya haka suma ‘yan Fim suke da su, wani lokaci ma har sun fi wasu ‘yan siyasar magoya baya ma’ana wadanda suke son su tsakanin da Allah.

Su kuma ‘yan Fim wannan ta ba su dama wajan kulla alaka da ‘ya ‘yan masu kudi da masu mulki da ‘yan siyasa da sarakuna da sauran jama’a, inda yanzu har ta kai ga cewa sun tsunduma cikin harkokin siyasa.

Siyasa mugun wasa! Idan baka shiga ba kar ka shiga idan ka shiga kar ka fita, haka dai masu iya magana suka fada, to yanzu ya ke nan, ‘yan fim sun tsunduma cikin harkokin siyasa inda har ake ganin suna wuce gona da iri.

Rashin shiga ko kusantarsu da gwamnati yasa a baya ana yi masu kallon masu gudun shiga a dama da su, amma da biri ya gane ashana sai gashi wankin hula na neman kai ‘yan Fim dare musamman arewacin Najeriya.
Wannan al’amari ba a Kano kadai yake faruwa ba yanzu ya kowa na kasa baki daya, lokacin da ‘yan Fim suka shiga uku a hannun gwamnati Malam Ibrahim Shekarau sun yabawa aya zaki, sannna suka yi karatun ta nustu wajan shiga harkokin gwamnati domin ko ba a dama da su ba, to sun tsallake wulakanci wani lokaci.

Hakan kuwa ya bada natija a lokacin da suka goyi bayan tsohon gwamna jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwanso kuma aka yi sa’a ya samu nasara sake komawa akan karagar mulki.
Sun sakata sun wala, sakamakon nasarar da kwankwaso ya samu, sannan wannan ce damar da suka yi amfani da ita suka kara fadada alakarsu da sauran ‘yan siyasa na wasu jahohi domin ance idan gemun dan uwanka ya kama da wuta shafawa naka ruwa.
Kafin kace kwabo ‘yan Fim din hausa sun mamaye kowace gwamnati a matakin tarayya da jahohi tare da kananan hukumomin domin ko ba komu su ke bada kudi domin sune suke da su, kuma saboda farin jinin ‘yan fim suna amfani da wannan damar wajan nemawa kansu jama’a musamman a lokacin yakin neman zabe.

Lokacin da zaben 2015 ya matso abin sai ya dauki wani sabon salo a lokacin ne a ke amfani da ‘yan Fim duk da cewar a baya ma anyi amfani da su, amma lokaci abin ya fi kamari ta inda duk lokaci da aka je yakin neman zabe sai ka ga an je da su saboda farin jininsu.

Wannan tasa ‘yan Fim suka mika wuyansu wajan ‘yan siyasa sannan masu kallonsu da gaskiya wadanda suke kaunarsu suka fara tunanin canza ra’ayinsu domin ko ba komi suna ganin masoyansu ga wani dan takara da ba su da ra’ayinsa, saboda haka sai matsala.
A bangare guda kuma ‘yan Fim suna samun kudin da ba su samun ko rabinsu a harkar Fim musamman da harka ta koma abin da ta koma, saboda yadda aka tsinci kai a wannan kasa na baki talauci da matsin tattalin arziki da har yanzu ba a fita ba.

Bayan da ‘yan fim suka samu wurin zama a wajan ‘yan siyasa sai suka fara canza launin tafiyarsu wajan nuna inda suka karkata koda yake ance hannu mai mai ake bi da lasa, to amma Bahaushi ya ce idan ana sara a dinga duba bakin gatari.

Daga cikin ‘yan Fim mawaka sun fi zakewa wajan nuna isa da cewa sune kan gaba, saboda sun fi kaudin baki da korara ‘yan siyasa sannan ana amfani da su wajan isar da sakon danne hakkin talakawa musamman da aka gano tasirinsu acikin al’umma da kuma yadda ake sauraransu.

Mutane irin su Rarara idan har aka samu canjin gwamnatin sune na sahun farko da za su fara yabawa aya zakinta, domin yanzu sun tashin daga inda aka san su sun kuma wani abun daban wanda ga alama wannan ba zai haifar da da mai ido ba idan aka samun canjin gwamnati.

Ankai wani matsayin da mutane irin su Rarara suna cewa duk wanda baya son wanda suke so, kamar ya fita daga Musulunci ne kuma ba su tare da shi duk da cewa siyasa ba da gaba ba ce.
Sun yi wakoki na cin mutunci da cin fuska ga wadanda suka canza tafiya da su, domin ance siyasa ai lissafi ce wasu kuma na cewa a a kasuwanci ce koma dai ya ya zaka ga cewa masu canza sheka suna da dalilinsu wadanda suka ki canzawa kuma suna da na su dalilin.
Tun ba a yi nisa ba, sai gashi irin abin da ake gudu ya fara faruwa domin kuwa bayan amfanin da wasu ‘yan siyasa suka yi da ‘yan fim ko mawaka wajan cin fuska da cin mutuncin wasu sai gashi an wayi gari sun kara hadewa a tafiya daya, to yanzu wa gari ya waya?
Haka duk irin laifin da ka aikatawa Najeriya inda kana cikin tafiyarsu to kai ba mai laifi bane amma da zaran ka canza tafiyarka saboda wani dalili da ko dai ba a san shi ba ko kuma an sanshi uziri ne ba za a yi maka ba, saboda kai baka cikin tafiya su wane.

Yanzu abu mafi muni da ke neman faruwa a tsakanin ‘yan Fim da mawaka shi ne har wasu jam’iyyun adawa na siyasa sun fara nuna wasu mawakan da yatsa suna cewa ana tattara kudadan jama’a ana mika masu alhali suma a baya sun yi irin haka wato sai yanzu suke jin haushin yadda abubuwan ke tafiya a halin yanzu

Kazalika har yanzu cikin ‘yan Fim babu wanda ya yi karatun ta nutsu wato ya koma cikin hayyacinsa ya yi sabon tuninin cewa yanzu idan aka samun canjin gwamnatin me zai faru da ni, kuma menene makomata?

Abubuwa da za su faru da ‘yan Fim idan aka samu canjin gwamnati suna da yawan gaske wanda sannu ahankali zan dinga kasu a wannan fili domin dai ko ba komi kila wasu su hankalta su dawo cikin hayyacinsu, ance don gobe ake wankan dare kuma da da mantuwa shege ne!

Daga Jaridar LeaderShipayau

Leave A Reply

Your email address will not be published.