Hawainiyarka Ta Kiyayi Ramar Baba Buhari – Sakon Iyaye Mata Ga Obasanjo

0 206

Hawainiyarka Ta Kiyayi Ramar Baba Buhari – Sakon Iyaye Mata Ga Obasanjo.
Hawainiyarka ta kiyayi ramar Baba Buhari – Sakon Iyaye Mata ga Obasanjo
Daruruwan Mata a jiya Laraba,8 ga watan Agusta sun gudanar da wata zanga zangar nuna goyon baya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar Legas, inda suka ja kunnen tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da ya fita daga idanun Buhari.
Daily Trust ta rawaito cewar ,shugabar kungiyar Africa women Arsie for Change, Josephine Okpara ce ta jagoranci wannan zanga zangar,inda mata dauke da takardu masu kunshe da jawabai daban daban suka dirarwa tashar yanci dake Ojota ta jihar Legas.
Okpara tace:“Mun shirya wannan zanga zanga ne domin tunawa jama’a da kada su yarda shuwagabannin da suka yi kokarin lalata Najeriya a baya su samu nasara, shuwagabannin na son yi amfani ne da yaki da rashawa wajen tunzura jama’a.”
Mrs Okpara ta kara da cewa shugaba Buhari ya nuna jarumta ta yadda ya sauya al’amari a tsarin shugabancin Najeriya, haka zalika tace yaki da rashawa da Buhari ya kaddamar ya kwato makudan kudade daga hannun barayi.
Bugu da kari Okpara ta gargadi tsohon shugaba Obasanjo da ya fita daga harkar Buhari, tunda dai shi ya gagara yaki da barayin gwamnati a lokacinsa, tace Obasanjo na amfani da damar mukamin da ya taba rikewa a baya ne wajen cin dunduniyar gwamnatin Buhari, sakamakon kishin Buhari ke yi na kawo canji a kasar nan, wanda shi bai yi ba a lokacinsa.
“Da ace Obasanjo ya yi shimfida mai kyau a zamaninsa, da Najeriya ta wuce matsayin da take ciki, salon mulkin da Obasanjo ya nuna a zamaninsa yayi ma Najeriya mummunan illa, hakan ya sanya Buhari yake fara komai sabo.”Inji ta
Hakazalika Okpara ta yi kira ga shugaban kasa da kada ya shakkar Obasanjo, ya kamata yakaddamar da bincike akansa, sa’annan kada ya karaya da barazanarsa, ya cigaba da yaki da rashawa tare da kama barayin gwamnati.Daga karshe Okpara ta jaddada goyon bayan kungiyarsu ga shugaba Buhari, tare da aminta da ireiren ayyukan cigaba da yake gudanarwa, sa’annan ta yi kira gareshi da ya cigaba da samar ma yan Najeriya romon Dim.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.