HOTUNA: Sojoji Sun Sake Kashe `Yan Shi`A Sama Da Dari Yau A Mararaba- Nyanya Abuja

0 179

Sojoji Sun Sake Kashe ‘Yan Shi’a Sama Da Dari Yau A Mararaba- Nyanya Abuja

Daga Bilya Hamza Dass

Bayan abinda ya faru ranar Asabar tsakanin ‘yan Shi’a da Rundanar Sojojin Nijeriya a gadar Zuba me nisan kilomita kadan zuwa Abuja, inda aka samu asarar rayuka da dama daga bangaren Shi’a, daga bangaren Sojojin ma sun fidda wasu hotuna dake dauke da Sojojin da suka ce ‘Yan Shi’an ne suka raunata.

A yau ma sojojin sun sake bude wuta kan ‘yan Shi’a inda har zuwa kammala wannan rahoton ba a tantance adadin rayukan da aka kashe ba.

Saidai wasu rahotanni sun nuna cewa an kashe mabiya Shi’a sama da dari wadanda suka hada yara da mata.

Hakan ya faru ne a daidai Nyanya dake daf da shiga babban birnin tarayya Abuja, inda dubban tawagar ‘yan Shi’a suka nufi shiga Abuja Sojojin suka dakatar dasu. Ga wasu daga hotunan yadda abin ya faru.

Leave A Reply

Your email address will not be published.