Hotunan Zuwan Shugaba Muhammadu Buhari Jihar Bauchi

0 374

Hotunan Zuwan Shugaba Muhammadu Buhari Jihar Bauchi.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa jihar Bauchi domin jajantawa wadanda gobarar da aka yi a kasuwar garin Azare ta shafa da kuma bala’in guguwa a jihar.

Shugaban ya isa jihar da ke arewa maso gabashin kasar ne a ranar Alhamis da safe.


  • A ranar Asabar ne aka yi wata mummunar guguwa a jihar wacce ta yi sanadin mutuwar mutum tare da jikkata wasu da dama, ta kuma lalata dukiyoyi.
  • Bayan wannan iftila’i ne kuma wata mummunar gobara ta tashi a babbar kasuwar da ke garin Azare na karamar hukumar Katagum a ranar Lahadi da daddare.

  • Bayan da ya sauka a garin Bauchi, shugaban ya wuce garin Azare ne inda ya fara kai ziyara fadar Sarkin Katagum kafin ya kai ziyara kasuwar Azare.


Dubban magoya bayan shugaban ne suka yi masa maraba.

  • Wani magoyin bayan shugaban rike da hotonsa cikin annashuwa.
https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.