Hukumar WAEC Ta Mika Wa Shugaba Buhari Takardar Shaidar Kammala Karatun Secondary

0 151

Hukumar da ke shirya jarabawar gama manyan makarantun sakandire ta kasashen yammacin Afirka (WAEC) wacce ta ke da ofishin ta a kasar Ghana ta mika wa shugaban kasa Buhari takardar shaidar kammala makarantar sakandire a yau Juma’a
Rajistran hukumar ne Dakta Iyi Uwadiae, ya mika wa shugaban kasar takardar shaidar a fadar shugaban kasar ta Villa dake Abuja, cikin mutanen da suka halarci mika takardar shaidar akwai sakataren gwamnatin tarayya Mista Boss Mustapha, ministan ilimi Malam Adamu Adamu, da sauran makarabban shugaban kasan.

A kwanakin baya an rawaito cewa shugaban kasan ya shaida wa hukumar zabe mai zaman kanta cewar takardun kammala karatun shi suna hannun hukumar soji, wanda hakan da jawo cece-kuce, har jam’iyyar PDP ta kalubalanci shugaban kasar da ya kawo takardun shi in da gaske yana da su.

Leave A Reply

Your email address will not be published.