Hukumar Yan Sanda Na Neman Ummi ZeeZee Kan Kazafin Da Ta Yi Wa Zaharaddeen, Sani Danja Da Fati

0 263

Idan ba a manta ba Ummi Zeezee ta rubuta a shafinta ta Instagram cewa Allah ne yayi wa Sani Danja, Zaharadden Sani, Fati Mohammed, Imraannan Mohammed gyadar dogo da tuni sun dade a garkame ofishin DSS a Abuja.

Ummi Zeezee ta koka ne cewa dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar ya aiko wa magoya bayan sa da ke farfajiyar finafinan Hausa da kudade masu yawa inda suka kebe kan su suka raba kudin ba tare da sun aika mata da kaso mai tsoka ba.

A shifidaddiyar wasika da ta rubuta inda ta jero sunayen wadanda take nufi da sakon nata ya iske su ta ce dukkan su sunci arzikin mahaifiyar ta ce da ta roke ta da ta yi hakuri da yanzu Sani Danja, Fati Muhammed, Zaharaddeen Sani, Alamin Buhari da Darekta Emrana sun dade a garkame a ofishin SSS a Abuja.

PREMIUM TIMES ta ji daga bakin Sarkin Yakin Atiku, Zaharadden Sani inda ya karyata korafin Ummi ZeeZee yana mai cewa ruwane ya kare wa dan kada.

” Abin da Ummi ZeeZee ta fadi maganganu ne da basu da madafa ko tasiri. Ummi ZeeZee ta yi barazanar sai ta daure mu saboda ta fi mu kafa a kasar nan. Ina so in sanar mata cewa mu da Allah muka dogara ga ba kafa ba kamar yadda ita ta ke takama da.

” Bayan nan ina so in sanar mata cewa ‘yan Sandan Najeriya na neman ta ruwa a Jallo domin tuni na nemi ta bayyana a kowani ofishin ‘yan sanda dake Kaduna domin ta tabbatar da korafin da ta yi cewa wai an bamu miliyoyin kudi mu kuma mun danne kudin. Idan ba ta bayyana ba ta sani an ba da takardar iko na duk inda aka ganta a kamata. Lallai ba za mu yadda ta ci mana mutunci ba mu kuma mu zuba ido kimar mu a idanun mutane ya zube. Sai dole ta zo ta fadi wanda ya bamu kudi sannan nawa aka bamu da ta ke cewa wai mu barayi ne.

” Wannan taro da muka yi a Kaduna, Taro ne da muka hada kuma mun samu halarcin manyan ‘yan jam,’iyyar PDP da ya hada da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki. Bayan an kammala taron ne, na zo fita sai na hangi Ummi ZeeZee a bakin kofar shiga. Muka gaisa na wuce.

“Ina isa dakin Otel dina sai ta kira ni ta ce wai yaya taro, sannan ta ce min me zata samu ne. Na ce mata ta turo wani in bata kudin Kati daga aljihuna a matsayin ta wanda na sani. Ta turo wani dan-uwanta na bata naira 25,000. Kafin kace wani abu, kawai ta tafi shafin Instagram ta ta rika zazzago magana.

” Ina so ta sani cewa mu ba irin wadanda za ta ci wa mutunci bane sannan ta karkada ta wuce. Duk da cewa ta fadi wai tana da gata da kafa a kasar nan fiye da mu, da Allah muka dogara. Ana ta neman ta amma ta na gudu. Sai dai mun sami takardar iko na a kamata a duk inda aka ganta. Domin dole ta zo ta yi bayanin kazafin da ta yi mana sannan ta bayyana ko a ina aka bamu miliyoyin kudin da take zargin an bamu.

Sarkin Yakin Atiku Abubakar, wato Zaharadden ya kara da cewa ko a shirye shiryen su da gwagwarmayar da suke yi ta yi kan kamfen din Atiku, daidai da rana daya basu taba ganin Ummi a wannan waje ba har da shi wannan taron bata zo ciki ba sannan bada ita aka shirya shi ba.

” Haka ya sa ko a wajen ma bata amma ta fito tana ta zaro maganganun da ba haka ba. Wani abu da nake so in sanar da kai kuma shine Ummi fa ba ma ‘yar Kannywoood bace yanzu. Da dai ta yi Kannywood amma yanzu bata harkar ta a farfajiyyar. Yaushe rabon da ace wai ta yi fim ko an ganta tana shirya fim. Ko ana Maganan matan fim yanzu sai dai mata kamar su Hadiza Gabo, Rahama Sadau, Nafeesat Abdullahi, Fati Washa da sauran su amma ba dai Ummi ZeeZee ba. Saboda haka ina kira gareta da ta bayyana kanta ko ta kai kanta ofishin ‘yan sanda a Kaduna domin idan ba haka ba duk inda aka ganta za a kamata. Domin kuwa sai ta gaya mana a ina muka yi sata, da ta kira mu barayi sannan wa ya bamu miliyoyin kudin da ta ce mun ki bata.

Wasikar Ummi ZeeZee

” Zuwa ga Fati Mohd, Sani Danja, Zaharaddeen Sani, Al’amin Buhari and director eemrana

” A ranar JUMA’AR data gabata mai girma dan takaran shugaban kasa ta jam’iyar PDP Alhaji atiku Abubakar ya shirya wani taro da zaiyi da yan fim da kuma mawaka na kannywood dan gane da siyasarsa sai dai kuma Allah bai bashi ikon zuwa ba sai ya wakilta sir Bukola Saraki Wanda daya zo taron ya bada kyautan makudan kudi miliyoyi ga jarumai da kuma mawakan kannywood Wanda suke PDP suke kuma yiwa wazirin adamawa kamfen.

“Ammah sai gashi saboda son zuciya irin taku kuda na lissafo sunayenku kuka raba kudin a iya tsakaninku kawai ko wanne acikinku ya dau naira million hudu da rabi saboda zalinci tsantsa.

” To shi ai bukola sarakin ba ku kadai ya bawa kudin ba da zaku rabashi kawai a tsakanin ku shi cewa yayi ya bayar ga duk yan PDP na kannywood masu yin atiku wai ammah sai kuka fara kawo uzurin karya cewar wai acikinku ko wani mutum ya gaiyato mutum hamsin ne domin taron shiyasa kuka raba kudin a tsakaninku Wanda kuma karya ne ba wasu mutane hamsin hamsin da kuka kawo taron domin nima na je taron kuma a matsayina na babbar yar PDP mai manyan mukamai har biyu baku bani nawa kudin ba.

” Sai bayan an tashi daga taron ne na kira actor zaharaddeen sani awaya ina tambayar nawa kudin wai shine dan renin hankali ya aikomin da naira dubu 25k kawai sai kace ya daukeni yar jagaliyar siyasa koko ince ya daukeni matsiyaciya ko yar yunwa.

” Dan haka wannan wasika na muku ne domin in muku gargadi.

” Wallahi wallahi wallahi in aka sake hada taron daya shafi atiku abubakar kuka raba kudi bani aciki to duk sai na kulleku a DSS na abuja baza a barku ba har sai kun biyani kudina domin na tabbatar acikinku ba mai connection din da nake dashi a Nigeria kuma ko wannan kudin ma dakuka dannemin rabo na naso na rufeku duka shine danayiwa mamana waya na gayamata ta hanani tace rigima ba dadi in barku da Allah kawai zai sakamin shiyasa na rabu daku bawai dan ina tsoronku ba domin naga sauran mutanen da sukaje taron kuka hanasu hakkinsu tsoro ya hanasu magana.

” Dan haka acikinku in akwai dan iska to dan allah in an sake bada kyautan kudi akan siyasar atiku mutum yaci nawa yaga mezaifaru!macutan banza kawai!!

ina ne muke barayi. Ina tabbatar maka da haka

Leave A Reply

Your email address will not be published.