Idan An Karbo Dukiyar Al’umma Daga Barayin Gwamnati A Rika Tunawa Da TALAKA – Nasihar Dr Ahmad Ibrahim BUK

0 123

Idan An Karbo Dukiyar Al’umma Daga Barayin Gwamnati A Rika Tunawa Da TALAKA – Nasihar Dr Ahmad Ibrahim BUK.

A cikin karatun Hadisi da gidan Rediyon Dala FM Kano suke sanyawa da karfe 6:00 kowacce safiya, wanda Dakta Ahmad Ibrahim BUK ya ke gabatarwa, yau Laraba ya shawarci gwamnatin tarayya da, kada kacokam ta tattara dukkan manufofinta wajen kwato dukiyar sata dake wajen barayin gwamnati, a kuma manta da sauran manyan bukatun Talaka.

“Idan an kwato dukiyar sai a yi wa al’umma wani abu da zai dauke musu radadin rayuwa, a duba batun man fetur, abinci da lantarki. Domin kwato dukiyar sata ba aiki ne na lokaci guda ba, sai an dauki lokaci, wanda idan ba a duba sauran bukatun talaka sai lokaci ya kure ba a yi masa komai ba”.

“Su wadanda ake fadan da su sun mallaki dukiya gida da waje ba ruwansu da tsadar rayuwa, ba su san matsalar abinci ba, ba su san matsalar man fetur ba, ba su san matsalar rashin magani a asibiti ba. Don haka yana da kyau shima Talaka ya rika amfanar romon Dimokradiyya.

Shehin Malamin ya kirayi shugaban Kasa da Gwamnonin jihohi da su rika kiyaye albashin ma’aikata, wanda ko ba a rika ba su duk 25 ga wata ba a rika ba su 30 ga wata domin samun damar biyan bashin da ke kansu da kuma hidimtawa iyalansu.

A karshe Malamin ya yi Addu’o’in samun sauki da kuma yalwar arziki ga Najeriya.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.