Idan ‘Yan Najeriya Suka Bari Buhari Ya fadi, Zasu Yi Kuka Da Idonsu – Inji Adam A. Zango

0 183

Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango ya baiwa ‘yan Najeriya shawara akan sake zaben shugaban kasa, Muhammadu Buhari a zaben shekarar 2019 me zuwa.

Adamu a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinshi na sada zumunta ya bayyana cewa, tunda ya fara sana’arshi babu wani dan siyasa me ci ko wanda ya sauka da ya taba taimakamai da miliyan da ya ko dubu dari, neman na kanshi yake tukuru.

Ya kara da cewa, yana so ya baiwa ‘yan Najeriya shawara kuma zai yi wannan maganane bil hakki har cikin zuciyarshi ba dan wani ko wata ba.

Yace idan ‘yan Najeriya suka yadda Buhari ya fadi mulki to zasu yi dana sani amma idan suka sake zabenshi zasu dara har zuwa ranar da zai sauka daga mulki.
A karshen maganarshi yace, idan kunne yaji..

Leave A Reply

Your email address will not be published.