Ina Da Niyyar Yin Aure Inji Nafisa Abdullahi

0 262

Shahararriyar jarumar fina-finan Hausa Nafisa Abdullahi ta ce tana da burin yin aure kamar kowanne mutum kuma nan gaba masoyanta za su sha labari.

Jaruma Nafisa ta yi wannan albishir ne a hira da ta yi da BBC yayin wata ziyara ta musamman a ofishinmu na Abuja.

Nafisa wacce ta ce ta fito a fina-finai Kannywood da dama, na daga cikin jaruman da ke da farin jini sosai a fina-finan Kannywood.

Jarumar dai ba ta bayyana takaimaiman lokacin da za ta yi auren ba sai dai ta ce, “Aure kamar yadda nake fada kullum lokaci ne na ubangiji, amma kuma hade da niyya, ina da niyyar a raina amma lokacin nake jira.”

Da aka tambaye ta mene ne sunan tauraron kuma ko daya ne daga cikin jaruman fim?

Sai ta yi dariya kuma ta ba da amsa kamar haka: “Ba shi da suna. Mai rabo ne kawai yana gefe.”

Leave A Reply

Your email address will not be published.