Jakadan Najeriya Ya Nemi A Hana Masu Zaman Kashe-Wando Tafiya Saudiyya

0 140

Jakadan Najeriya Ya Nemi A Hana Masu Zaman Kashe-Wando Tafiya Saudiyya.

Jakadan Najeriya a kasar Saudiyya, Muhammadu ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta hana ‘yan Najeriya masu zaman banza tafiya ci-rani Saudiyya.

Ya ce akasarin su ba su da wata sana’a, sai sun je can ne su fara gaganiyar neman aikin a za su rika yi.

Ya ce idan har gwamnatin tarayya ta yi wannan kokari, ta hana su shiga Saudiyya, to hakan zai hana zubewar mutuncin kasar nan a idon uniya.

Modibbo ya yi wannan kira ne a Makkah, a lokacin da ya ke tattaunawa da wakilin Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, a Saudiyya.

“Tuni har na rigaya na aika da wasika zuwa ga Ma’aikatar Harkokin Waje a Najeriya, inda a ciki na yi kira da a hana ‘yan Najeriya tururuwar shigowa Saudiyya da sunan neman aiki, saboda banda bakar wahala da azaba. Babu abin da suke ci.

“Kuma su ma ‘yan Najeriya ina kara jan hankalin mu da su daure su rika tsayawa can a gida su na neman sana’ar da za su rika dogaro da ita, maimakon kokarin shigowa nan Saudiyya, domin wahala ce kawai, kuma kallon kitse su ke yi wa rogo daga nesa.

Ya kara da cewa ofishin sa na jakadancin Najeriya a Saudiyya ya damu sosai da yawaitar yadda matan Najeriya suke zuwa Saudiyya, su na barance da aikatau a gidaje, inda ake yawan cin zarafin su.

Ya kuma koka da irin yadda ake samun masu safarar kwayoyi daga Najeriya zuwa cikin Saudiyya.

Ya ce duk da irin yadda ofishin sa da kuma shi kan sa ke yawan sa baki wajen batun wadanda ake kamawa da manyan laifuka, musamman safarar kwayoyi, har yanzu akwai ‘yan Najeriya da dama ke a tsare, su na jiran a kaddamar da hukuncin kisa a kan su.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.