Jam’iyar APC Ta Soma Zawarcin Shekarau

Jam'iyar APC Ta Soma Zawarcin Shekarau

0 500

JAM’IYYAR APC TA SOMA ZAWARCIN SHEKARAU

Yau Juma’a Shugaban APC Na Kasa, Adams Oshiomhole Da Tawagarsa Za Su Ziyarci Shekarau Har Gidansa A Kano

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Aliyu Oshiomhole ya bada sanarwar zai ziyarci tsohon gwamnan Kano Mallam Ibrahim Shekarau a gidansa da ke Mundubawa gobe Juma’a da hantsi.

Zai kai ziyarar girmammawa ne ta musamman ga Sardaunan Kano.

Rahotanni sun ce Oshiomhole zai zo Kano ne da wata babbar tawaga ta sanatoci da ‘yan majalisar tarayya da wasu daga cikin ministocin gwamnatin tarayya.

Wannan ziyarar tana zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar PDP a jihar Kano ta shiga halin lahaula da shugabanta na kasa Cif Uche Secondus ya jefa ta sakamakon nuna bambanci tsakanin membobin jam’iyyar tun bayan da tsoffin membobinta ke rububin dawowa cikinta.

Leave A Reply

Your email address will not be published.