Jam’iyar PDP Tayiwa Tunibu Gargadi Akan Atiku

0 231

Zaka Gamu Da Fushinmu, Muddin Baka Daina Cin Mutuncin Atiku Ba – Gargadin PDP Ga Tinubu

Jam’iyyar PDP ta gargadi Bola Tinubu da kada ya kuskura ya shiga ‘yar tsama da kuma kamfen din batunci a kan dan takarar shugabancin jam’iyyar, Atiku Abubakar.

Kakakin Yada Labaran PDP ne, Kola Ologbondiyan ya bayyana haka a cikin wata takarda da ya raba wa manema labarai jiya Alhamis da yamma.

Ranar Laraba ne Tinubu ya bayyana cewa shirye-shirye da kulle-kullen da Atiku da tawagar kamfen din sa ke yi a Dubai komin kayar da Buhari a zaben 2019 ba zai yi nasara ba.

A yanzu dai Atiku da tawagar sa na Dubai su na tsara yadda za su hudo wa shirin yakin neman zaben 2019 da za fara tun daga ranar 18 Ga Nuwamba.

Tinubu ya ce ba su tsoron duk ma inda su Atiku za su ce su yi kulle-kullen su, ko a dokar daji, ko a Dubai, ko a Abu Dhabi.

Sai dai kuma PDP ta ce Tinubu fa dattijon jam’iyyar APC, don haka ya ja girman sa, kada ya karyar da mutuncin sa ya na tsoma baki a dukkan lamurran da ba su shafe shi ba.

Kola ya kara da cewa kamata ya yi Tinubu ya ja bakin sa ya yi shiru, dangane da lamarin Atiku, wanda ya ce tuni ‘yan Najeriya sun rigaya sun yanke shawarar cewa shi ne shugaban kasar su a 2019.

Leave A Reply

Your email address will not be published.