Jarumai 10 na KannyWood da suka fi kowa kudi

0 643
JARUMAI 10 NA KANNYWOOD WANDA SUKA FI KOWA KUDI.

Akwai dumbin jarumai da su ke da kudi a masana’antar kannywood sai dai mun duba mutane 10 da Su ka fi kudi a wannan shekara bisa dogaro da dalilai na zahiri.


1. Ali Nuhu shine jarumin daya fi kudi a kannywood, Ya na da gida a kano da hotal a bauchi , yana yiwa kamfanoni kimanin shida ko bakwai jakadanci Ya kai kimanin shekaru 15 ya na jan zare a matsayin jarumin jarumai a kannywood.

2. Adam A. Zango shi ne jarumi na biyu da ya fi kudi a taurarin kannywood, Ya kammala gina wani kasurgumin gida a kaduna , Ya na karbar miliyan daya da rabi idan an gayyace shi biki kuma akalla ya kan ziyarci irin bukukuwan sau uku a wata daya, sannan ya na karbar kimanim dubu dari uku kafin ya fito a fim kafin daga bisani ya daga zuwa dubu dari biyar , ya kan yi fina finai akalla hudu a wata daya, sannan shi jakadan kamfanin MTN ne a kowanne wata ya kan samu kudi daidai da kimar naira miliyan biyar.

3. Dauda Kahutu Rarara ya shiga jeri na uku cikin ma Su kudin kannywood , tun bayan zaben dabya gabata , Ya na da wani makeken Gida a zoo road kano.

4. Mawaki Nura M. Inuwa shine na hudu a lissafin wanda su ka fi kudi a kannywood , ya na fitar da albam biyu duk shekara, wanda su ke samar da kimanin miliyan 25, Ya kasance ya fi karkata a wakokin biki wadda bayanai sun nuna ya na karban dubu dari biyu da hamsin a kowacce waka, sannan a mako daya ya kan yi akalla wakoki biyar.

5. Halima Atete ita ce ta biyar a jerin wanda su Ka fi kudi a kannywood kuma ta farko a jarumai mata, ta dauki tsawon lokaci ta na shirya fina finai da kudinta.

6. Sani danja shine na shida a rukunin attajiran kannywood ya na da Gida a abuja, Ya samu makudan kudade a lokacin zaben 2011 inda ya rika taya shugaban kasa kampe a wanchan lokaci.

7. Sadik Sani Sadik shine na bakwai a jerin Wanda su Ka fi kudi a taurarin kannywood.

8. Nafisa Abdullahi ita ce ta takwas a cikin jerin attajiran kannywood kuma ta biyu a cikin mata, Ta na shirya fim na kashin kanta.
9. Hadiza Gabon ita ce ta takwas a rukunin attajiran kannywood.
10. Aisha Aliyu Tsamiya ce ta goma a rukunin taurarin attajiran kannywood.
https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.