Kalli Hotunan Ganawar Buhari Da ‘Yan Kannywood

KannyWood

0 427

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da wasu ‘yan wasan Hausa da mawaka da kuma samu shirya fina-finai daga yankin arewacin kasar a fadar da ke Abuja.

‘Yan wasan sun ba shi tabbacin samun goyon bayansa a babban zaben kasar wanda za a yi a shekarar 2019.

Cikin ‘yan wasan da suka halarci taron har da Rukayya Dawayya da Fati Shu’uma da Rashida Abdullahi da sauransu.

Ba wannan ne karon farko da shugaban ya fara shirya wa ‘yan wasan Hausa liyafa ba.

Sai dai wadansu na danganta wannan liyafar da gabatowar babban zaben 2019.

A lokacin da yake yi musu jawabi, Shugaba Buhari ya ba su tabbacin ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa a kasar.

Cikin wadanda suka samu halartar taron har da mawaka kamarsu Ali Jita da Naziru M Ahmad da Fati Nijar da Dauda Kahutu wanda aka fi sani da Rarara da sauransu.

Har ila yau akwai jaruman fina-finai kamarsu Hamisu Iyantama da Adam A Zango da Nura Husseini da Rabi’u Rikadawa da.

Shugaba Buhari ya samu goyon bayan wadansu daga cikin ‘yan Kannywood lokacin da ya lashe zaben 2015.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.