Kalli yadda atiku yace zai sayarda NNPC koh za’ayi kasheshi

0 246

Dan takarar shugaban kasar Najeriya a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa idan ya zama shugaban kasa za ya saida kamfanin man Najeriya, NNPC.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wani taro da ya yi da yan kasuwa a jihar Legas ranar Laraba.
Atiku ya ce “Zan tabbatar da sayar da NNPC ko da za su kashe ni.”
Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana wa BBC shakkunsa kan hukumar zaben Najeriya game da gudanar da sahihin zabe.

Ya ce akwai tambayoyi da ke bukatar amsa a game da wasu daga ma’aikatan hukumar zaben da ke da dangantaka da shugaban kasa da kuma tsarin katuttukan zabe da na’urori.


Atiku Abubakar dan kasuwan ne kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya tsakanin 1999 zuwa 2007.

A watan Nuwamban 2017 ne ya kaddamar da yakin neman zabensa da alkawarin cewa zai hada kan ‘yan Najeriya da samar da ayyukan yi.


Atiku Abubakar dai ya bar jam’iyar APC inda ya koma PDP a ranar 3 ga watan Disamba na 2017.
Wannan shi ne karo na biyu da zai yi takarar zaben game-gari tun bayan da ya sauka daga mataimakin shugaban kasar Najeriya a 2007.

Leave A Reply

Your email address will not be published.