Ko Yaushe NeAli Nuhu da Adam A Zango Zasu Dena Rikici.

Yaushe NeAli Nuhu da Adam A Zango Zasu Dena Rikici

0 329

Ali Nuhu da Adam A. Zango, ko kuma Sarki Ali da Prince Zango – kamar yadda aka fi sanin su a Kannywood – mutane ne masu matukar hazaka.

Baya ga basira, ‘yan wasan na Kannywood na da magoya bayan da babu wani a masana’antar ya mallaka.

Sai dai ba magoya baya suka fi kowa kawai ba – sun fi kowanne dan wasan Kannywood yawan “munafukai” da ke kusa da su.

Watakila hakan ne ya sa suka fi ko wadanne ‘yan wasan Kannywood yawan rikici a tsakaninsu.

Tambayar da kowa ke yi ita ce su wane ne wadannan mutane da ba sa so a zauna lafiya tsakanin fitattun jaruman na Kannywood? Kuma yaushe za su daina rikici

Adam A. Zango, wanda ya wallafa wasu hotunansa a shafinsa na Instagram tare da Ali Nuhu ranar Asabar da daddare bayan sun kwashe wata da watanni suna “gaba”, bai bayyana sunayen munafukan ba.

“Karshen munafukai…mai wuri ya dawo…Allah ina godiya da irin wadannan jarabtar da ka yi min,” in ji Adam A. Zango.

https://www.instagram.com/p/BnM0oo3lQIG/?taken-by=adam_a_zango

Wannan dai sako ne mai cike da bayanai ga duk mutumin da ya san masana’antar Kannywood kuma ya san yadda Adam Zango ba ya yi wa bakinsa linzami.

Sai dai duk kokarin da muka yi domin samun karin bayani kan wadannan kalamai daga bakinsa ba mu yi nasara ba.

Kazalika makusantan jarumin sun ce ba su san “munafukan” da ke shiga tsakanin sa da Ali Nuhu ba.

“Wallahi ban san su [munafukan] ba,” a cewar babban aminin Adam Zango, Malam Falalu Dorayi, a sakon da ya aike min na text.

Wannan layi ne

Rayuwar Ali Nuhu a takaice

  • An haife shi a watan Maris na 1974
  • Ya yi karatun firamare da sakandare a birnin Kano
  • Ya yi digiri a jami’ar Jos, kuma ya yi hidimar kasa a jihar Oyo a 1999
  • Ya fito a fina-finai sama da 100 na Hausa da Turanci
  • Yana cikin Hausawa na farko-farko da suka fara fitowa a fina-fina Nollywood
  • Ya shahara matuka a fagen fim a ciki da wajen Najeriya
  • Ya ci lambobin yabo da dama, abin da ya sa ake masa lakabi da Sarki

Amma Malam Muhsin Ibrahim da ke nazari kan fina-finan Kannywood kuma yake koyar da su a Jami’ar birnin Cologne ta kasar Jamus, ya shaida min cewa magoya bayan jaruman ne ke hada su fada.

“A takaice, magoya bayansu ne ke hada su rigima, kowa yana neman gindin zama.”

Ba kamar Adam A. Zango ba, Ali Nuhu, ba ya fitowa fili ya bayyana wata rashin jituwa tsakaninsa da abokin aikin nasa.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.