Kotu a Tsare Wani makiyayin da shanunsa suka yi asarar hatsin Naira miliyan 4

0 109

Hukumar ‘yan sandan  Abeokuta babban birnin jihar Ogun ta gurfanar da wani makiyayi dan shekara 40 mai suna Usman Abubakar akan laifin lalata wa wasu manoma hatsin gonakinsu da ya kai Naira miliyan 4 da shanun sa suka yi.

An dai gurfanar da makiyayin ne a kotun Majistiri da ke Abaokuta akan laifuka uku da ake tuhumarsa.

Jami’in dan sandan da ya shigar da karar sufeto Olubisi Lawrence ya bayyana wa kotun cewa, makiyayin ya aikata laifin ne a ranar 10 ga Oktoba 2018 da misalin karfe 5:00 na yamma a kauyen Alagbagba a Abeokuta.

Leave A Reply

Your email address will not be published.