Ku Zabi Jam’Iyar APC Daga Sama Har Kasa, Cewar Matar Gwamnan Bauchi – Hajiya Hadiza M. A

0 146

Uwar Gidan gwamnan Bauchi, Hajiya Hadiza M. A Abubakar ta bukaci al’umar yankin Arewa maso Gabas da su sake zaban shugaba Muhammad Buhari da dukkan ‘yan sauran ‘yan takarar a jam’iyar APC.

A wata sanarwa da ta fito dauke da sa hanun mai taimakawa gwamnan jihar kan Sadarwa, Shamsuddeen Lukman Abubakar ya bayyana cewa, Mai Dakin gwamna Muhammad Abubakar ta bayyana haka ne a yayin kaddamar da gangamin mata da mata na yakin neman zaben shugaban kasa Muhammad Buhari, yankin Arewa maso Gabas da aka gudanar a birnin Bauchi.

Hajiya Hadiza ta bukaci al’uman yankin da su zabi Buhari, da kuma ‘yan jihar Bauchi su zabi gwamna Muhammad Abdullahi da sauran ‘yan takaran APC domin ci gaba da aiyukan alkhairi da suka fara yi musu.

Mai dakin gwamnan, kuma ita ce jagorantar tawagar mata da matasa a Arewa Maso Gabas, na sake neman zaban Muhammadu Buhari ta ce ta na da tabbacin mata da matasa na yankin su na bayan jam’iyar APC da shugaban kasa dari bisa dari.

Uwar gidan shugaban kasa Aisha Buhari, wanda uwar gidan mataimakin shugaban kasa Misis Dolapo Osinbajo ta wakilta ta bayyana godiya da jin dadinta ga al’uman yankin, musamman jihar Bauchi bisa yanda suka nuna goyon bayansu ga Buhari da jam’iyar APC. Ta ce jihar ta Buhari da matarsa.

Daga karshe ta mika godiyarta ga Hajiya Hadiza Muhammad bisa kokarinta na tallafa wa rayuwar mata da yara a jihar, inda ta ce kokari irin nata zai taimaka wa jam’iyar APC.

Taron ya samu halartan kungiyoyin mata da matasa daban daban daga sassan yankin ta Arewa Maso Gabas da wasu manyan kasa da jam’iya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.