Kwankwaso ya nemi PDP ta tsayar da shi takarar shugaban Nigeria

0 214

Kwankwaso ya nemi PDP ta tsayar da shi takarar shugaban Nigeria.

Tsohon gwamnan jihar Kano da ke arewacin Najeriya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce zai nemi jam’iyyar PDP ta tsayar da shi takarar shugabancin kasar.


A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Sanatan da ke wakiltar Kano ta Tsakiya a majalisar dattawan kasar, ya ce ya dauki wannan mataki ne bayan ya gana da mutane da dama.
“Bayan na yi gagganawa, na dauki matakin neman tsayawa takarar shugabancin Najeriya karkashin jam’iyyarmu ta the People’s Democratic Party,” in ji dan majalisar.
A watan Yuli ne Sanata Kwankwaso da wasu ‘yan majalisar dattawa da ta wakilai suka fice daga jam’iyyar APC mai mulki suka koma PDP.
Sun bayyana cewa APC ba ta yi musu adalci ba duk da fafutukar da suka yi wajen ganin ta yi nasarar cinye zaben shugaban kasar a 2015.
Sai dai shugabannin APC da ma Shugaban kasar Muhammadu Buharu sun ce ‘yan majalisar sun yi gajen hakuri, suna mai cewa fitar su daga jam’iyyar ba zai hana ta cin zaben 2019 ba.
Sanata Kwankwaso – wanda sau biyu yana zama gwamnan jihar Kano – zai fafata da jiga-jigan ‘yan siyasa da ke neman PDP ta sayar da su takara a zaben 2019.
BBChausa
https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.