Kwankwaso Zai Yi Gangamin Kaddamar Da Takarar Shugaban Kasa A Abuja

0 198

Kwankwaso Zai Yi Gangamin Kaddamar Da Takarar Shugaban Kasa A Abuja.


Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa zai gangamin kaddamar da takarar shugaban kasa a Abuja ranar Laraba.
Binta Sipikin ta bayyana haka a takarda da ta saka wa hannu a madadin Kwankwaso.
Sipikin ta ce babban dalilin da ya sa za a yi kaddamarwar a gari Abuja shine don nan ne mahada.
” Abuja ne babban birnin tarayyar Najeriya sannan mahada. Tunda takarar na kasa ne kowa ya taso Abuja zai fi masa saukin zuwa.
” Taron ba ta Kano ba ce, taro ne da ya shafi kasa baki daya, shine yasa muka zabi muyi a Abuja.” Inji Sipikin.
Za ayi taron ne ranar Laraba, a filin Eagle Square dake Abuja
https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.