LAIFI NA DAYA DA NAYI SULHU DA ADAM A ZANGO INJI WANI FURODUSA

0 217

Da alama tsugunne bata kare ba a masana’antar film ta kannywood domin furodusa Alhaji sheshe yayi wadansu kalamai na nuna cewa har yanzu kura bata lafa ba a rikicin da ake yi tsakanin wasu magoya bayan Ali nuhu a acikin masana’antar kannywood da Adam A zango,

Alhaji sheshe yayi zargin ana ci masa fuska da habaici saboda kawai yayi sulhu da adam a zango, wanda yanzu haka ana hasashen gabar da take tsakanin Ali Nuhu da zangon tana nema ta dawo.

Habaici da gulmace-gulmace abu ne wanda aka riga aka saba dashi musamman a masana’antun fina-finai, sai dai a kannywood zamu iya cewa abun yafi na ko’ina. Gadai abunda furodsan ya rubuta a shafinsa na sada zumunta:

” Laifi na daya ne da naje nayi SULHU da Adam a zango.

ALLAH SWT YACE A CIKIN ALQUR,ANIN SA MAI GIRMA (WASSULHU KHAIR)

ANNABI SAW YACE KU YAWAITA SULHU DOMIN ACIKIN YIN SULHU AKWAI ALKHAIRAI MASU YAWA.

Duk wanda Yake Ganin Banyi Daidai ba sbd nayi SULHU Yazo ya kawo min Hujjar sa da take Hanayin SULHU a cikin Addini na Na MUSULUNCI ko kuma A cikin Addinin Makota na Na KIRISTANCHI.

FILM din Hausa Shine Sana,a ta kuma shine Abinda MALA,IKU zasu Tambaye Ni akai Idan ALLAH yayi Ikon sa akai na An sakani a QABARI.

Ina so na Fadawa MALA,IKUN da zasu Tambaye ni Hujja ta tayin Sana,ar Film kuma Ina so Allah ya bani Ikon tsaftache sana,ar ta yadda zan kyautata Muamala ta da mutane kuma Na tsaftache nema na a cikin sana,ar Ta Yadda Allah zai bani ikon chin HALAK YA ALLAH kasa wannan Sana,ar da nake ta zamto sanadiyyar cin HALAK dina.

Ni Dan ADAM NE kuma duk dan Adam AJIZI NE zai iya yin Laifi a baya kuma zan iya yi anan gaba AMMA a yanzu Ina ROKON ALLAH yasa Abinda Nayi ya zauto Mafi Alkhairi a tare da RAYUWA TA.

Bana TSORO KUMA BANA JIN Tsoron Dan ADAM ALLAH SWT SHI nake Tsoro sbd shine yake da Ikon yin komai akai na a kuma duk LOKACHIN da yaga dama.

Ko ka zage ni ko ka aibata ni duk babu Abinda zai dame ni sbd Ni ba MA,ASUMI bane ANNABI SAW ya rayu da Mutane kuma ya fuskanchi QALUBALE a Rayuwar MANZAN CHIN SA.

Wane ne NI? NI mutum ne Me yawan sabawa MAHALICCHI NA me yasa zanyi tunanin bazan samu QALUBALE A RAYUWA TA BA?

SHAHIDU NI JAMI,AN THUMMA LA TUN ZEERUN.

KUYI MIN KAIDI GABA DAYAN KU IDAN ZAKU IYA. AMMA KU SANI BAZA KU IYA KARYA NI KO KU SA ABINDA ALLAH YA QADDARA A KAINA YAQI FARUWA A KAINA BA.

Ya ALLAH KA ZABA MIN ABINDA YAFI ALKHAIRI A RAYUWA NA YA ALLAH KASA RANAR MUTUWA TA TA ZAMTO RANAR ALFAHARI A GARE NI

Leave A Reply

Your email address will not be published.