Mafusatan Matasa Sun Lalata Allunan Kamfe Din Buhari A Jihar Kano

0 153

Mafusatan Matasa Sun Lalata Allunan Kamfe Din Buhari A Jihar Kano
Mafusatan matasa sun lalata allunan kamfe din Buhari a jihar Kano
Jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya dake jihar Kano ta fitar da sanarwa tare da kakkausan kashedi ga dukkan masu lalata hotuna da kuma allunan kamfe din shugaba Buhari a jihar.
Mai magana da yawun ‘yan sandan na jihar, Musa Majiya ya ce wannan ya zama tilas domin irin yadda mummunar dabi’ar da suke zargin ‘yan adawa ne ke yinta ke neman zama ruwan dare a jihar.
A cikin sanarwar dai ‘yan sandan sun ce sun samu labarin yanzu haka ma wasu bata garin sun lalata allon kamfe din Buhari dake kan titin Sharada kuma sun sha alwashin hukunta duk wanda suka samu da laifin.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.