Magauta Sun Kaiwa Mawaki Ado Gwanja Farmaki Har Office Dinsa

Ado Gwanja

0 228

A Ranar Talata 2 Ga Watan October Wasu Matasa Kimanin Mutum 8 zuwa 10 Sunkaiwa Mawaki Ado Gwanja Farmaki Har Cikin Office Dinsa Da misalin Karfe 8:00 na dare.

Wadannan Matasa Dai Sun Shiga Office din mawakin ne yayinda Suka nuna Suna Neman mawakin, Saidai Sunyi Rashin Sa’a Domin Kuwa Ado Gwanja bayanan a lokacin, ganin Basu sameshi a Wannan lokacin ba shine Suka fara zage zage suna fito da makamai Akan saisun farmaki mawakin.

Dayake Office Din mawakin wajene mai ciki da Jama’a ai Kuwa nan Da nan Jama’a suka cika wajen Domin Kokarin daukar mataki akai.

 

Bayan wadannan yan jagaliya sunga Mutane sunyo kansu Sai Suka ranta ana kare amma daga bisani anyi sa’ar kama mutum biyu daga cikin su.

Ba’a wani bata lokaci ba aka sanar da hukumar yan sanda sukazo suka tafi da wadannan mutane biyu da aka kama.

Mun tuntubi manajan Mawaki Ado Gwanja wato Bello Vocal Akan cewa ko Zaiyi mana wani Karin haske Saboda ganin Akan idon Sa Wannan Abu Yafaru, Sai yace shima dai bashida wata Masaniya Amma Tunda case yaje hannun hukuma idan da wani Karin bayani zamuji daga baya.

Amma wasu daga cikin Wanda Abun yafaru a idonsu Suna zargin sharrin makiyane Musamman ma ganin yadda Bikin mawakin ya karato.

Leave A Reply

Your email address will not be published.