Mai neman kujerar shugaban kasa ya roki yan Nijeriya da su tallafa masa da kudin siyan takardan tsayawa takara

0 347

Wani dan jam’iyar adawa ta PDP kuma mai neman tsayawa takarar kujerar shugaban kasa Hamidu Tafida yayi kira ga yan Nijeriya da sy tallafa masa da naira 200 domin siyan takardar tsayawa takara na jam’iyar sa
.
.
Yayi wannan kiran a jihar Taraba ranar asabar 1n ga watan Satumba yayin da ya kaddamar da kansa cikin masu neman haye kujerar shugaban kasa a zaben 2019
.
.
Yana mai cewa “Ina mai kira ga yan Nijeriya miliyan daya da su taimaka su hada mun naira dari biyu domin in siya takardar tsayawa takara domin aiwatar da anniyar ta don amfanin kowa”
.
.
Yace lokaci yayi da yan Nijeriya zasu fita da kunci rayuwa da suke fuskata a halin yanzu
.
.
Hamidu Tafida zai kara da sauran jiga-jigan jam’iyar PDP da suka kaddamar da anniyar su na tsayawa takarar kujerar shugaban kasa
.
.
Za’a gudanar da zaben jam’iyar domin tabbatar da gwani wanda zai daga tutar jam’iyar a zaben 2019 nan bada dadewa ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.