Majalisa Ta Bukaci A Soke Cajin ATM Da Bankuna Ke Yi

ATM

0 256

Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci babban bankin kasar CBN da ya soke cajin cire kudi ta amfani da injin cire kudi ‘ATM’ da bankuna ke yi wa abokan huldarsu daga cikin asusun ajiyarsu.

Majalisar ta ce, cajin kudin da ake yi wa abokan huldar daga bankuna idan sun cire kudi sama da sau uku a wata ta hanyar amfani ATM bai dace ba

Sanata Gbenga Ashafa daga mazabar jihar Legas ne ya gabatarwa zauren majalisar korafin jama’a. Ya kuma bukaci bankuna su tsara yadda injin ATM zai iya fitar da kudi da ya kai naira dubu 40 lokaci guda.

Leave A Reply

Your email address will not be published.