Manazarta: Duk Talakan Da Bai Zabi Buhari Ba Bai San Ciwon Kansa Ba

0 155

Wasu matasa masu bibiya gami da binciken ayyukan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a jihar Kano, Aliyu Habibu Gwarzo, tare da Habibu Sani da suka kudiri wayar da kan mutane domin wayar da kan mutane akan ayyukan raya Kasa da ake yi na ci gaba da kuma ci gaban tattalin arziki. Sun jaddada cewa duk talakan da bai zabi Buhari ba bai san ciwon kansa ba. Matasan sun yi wannan batu ne a wani shiri da suka kaddamar mai suna ‘DON TUWON GOBE’

“Dalilin da ya sa muka kudiri bincike akan ayyukan Buhari saboda sukar sa da ake yi ya fi aiki Kudu akan Arewa. Baba wata jiha daya da Buhari ya ware ita kadai ya ke mata aiki, Buhari Najeriya ya ke yi wa aiki ba jiha ba.

Amma ance titunan da ya ke yi a Kudu babu irinsu a Arewa? Idan ka duba titunan da ake magana a da muka yi bincike a record sun ba da titi 365 wanda 121 gado su aka yi daga gwamnatin baya, ragowar ne sabbi, kuma kowane idan aka duba ci gaban Najeriya ne ba na wata jiha kadai ba.

Ko titunan da ake yi a Kudu mutanen Arewa ake taimakawa. Saboda kusan kaso 80 na kayan da muke amfani da su daga Kudu ake kawo mana. Kuma ba mutum daya ne zai amfana da titunan ba, zai taimaka wajen ci gaban kasa da tattalin arziki. Sannan babu wata jiha da Buhari bai ba wa mukamai sama da goma ba. Shugaban kasa ba shugaban Kano ba ne ko Shugaban Kaduna ko Jigawa Shugaban Najeriya ne, ayyukan da ya ke don kasa ya ke yi ba don jiha ba.

Me ya sa masu fadin maganar ba sa sukar cewa an yi gidan wuta a Mambila ba a yi a Ogun ba? Me ya sa ba a sukar janyo bututun mai daga Nijar zuwa Kaduna ba? A baya Naira miliyan uku ta ke sa wa a asusun jarabawar Jamb, amma yanzu a lokacin Buhari Naira Biliyan Takwas aka samu. PDP ta ce duk jihar da ta ke da mai ita za ta rike abinta sai dai su rika bayar da haraji, kenan wadanda ba su da mai bara ake so su yi?

Kwanan nan Buhari ya biya ma’aikatan Nigerian Airways wanda shekara sama sama da goma sha sun kasa biya. A baya wutar lantarki megawas 4,000 ne amma yanzu megawas 7,000 ne da mu.

Najeriya ce a gaban Buhari ba tara dukiya ba, bai zama rariya da dukiyar kasa za ta zurare ba. Dole mu fahimtar da mutane su yi kishin kasa su ajiye kabilanci mu so juna, ba wai kawai a kwashe dukiyar Kasa ba. Daga kin gaskiya sai bata, jama’a su dubi abinda Buhari ya ke yi tsakani da Allah

Mu yi kokarin fada da cima-zaune, abinda Buhari ya fada gaskiya ne, dole mu tashi mu yi kishin kasa, mu yi amfani da ilimi mu tashi mu jajirce mu nemawa kanmu da kasar mu mutunci a idon duniya ta hanyar da ya dace.

Leave A Reply

Your email address will not be published.