Marigayi Shagari yana aljannah – Sarki Sanusi II

0 114

– Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya ce tsohon Shugaban kasar Najeriya Shehu Shagari yana aljannah Firdausi.

– Sarki Sanusi II ya fadi hakan ne yayin jawabin da ya yi a garin Sakkwato lokacin da ya tafi ziyarar ta’aziyya ga iyalan mamacin – Sarkin na Kano ya kafa hujja da ayoyin Al-Kurani mai tsarki da suka ce daga cikin alamar dan aljannah shine samun shaidan alheri bayan mutuwar mutum Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammad Sanusi II tare da wasu manyan ‘yan Najeriya sun bayyana cewa rasuwar tsohon shugaban kasar Najeriya, Shehu Usman Aliyu Shagari babban rashi ne ga kasar a yayin ziyarar ta’aziyar da suka kai a Sokoto. Sanusi ya kara da cewa ya yi imanin cewa marigayi shugaban kasa Shagari yana gidan aljanna duda da irin ayyukan alheri da rayuwa da gari da ya yi, ya ce marigayin bashi da girman kai ko kadan.

Sarkin ya karanto wasu ayoyin Al-Kur’ani mai girma domin ya kare abinda ya fada inda ya ce shaidan alheri bayan rasuwar mutum alama ce da ke nuna mutumin zai shiga aljanna Firdausi kamar yadda Leadership ta ruwaito. A bangarensa, Jagoran jam’iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu ya ce za a rika tunawa da Shagari a matsayin mutumin mai son hadin kai da zaman lafiya da kuma goyon bayan demokradiya.

Tinubu ya ce, “Ni da iyalai da mutanen jihar Legas mun kasance cikin bakin ciki yayin da muka samu labarin rasuwar tsohon shugaban kasa, Shehu Usman Aliyu Shagari, ina son amfani da wannan damar domin mika ta’aziyyar mu ga iyalansa.” A jawabin da ya yi a madadin iyalan marigayi Shagari, babban dansa, Alhaji Bala Shehu Shagari ya mika godiyarsa ga dukkan wadanda suka zo ta’aziyar da wadanda suka aike da sakonni.

Marigayi Shagari yana aljannah – Sarki Sanusi II

Source: Depositphotos

Leave A Reply

Your email address will not be published.