Maryam Both ta Jinjinawa Sojojin Nigeria a Wani Yanayi na Burgewa

0 412

Maryam Both ta Jinjinawa Sojojin Nigeria a Wani Yanayi na Burgewa.

Kokari da sadaukarwar Sojojin Najeriya ba zata tafi a banza

– Jarumar Fina-finan Hausa ta jinjina musu kan irin gudunmawar da suke bayarwa

Shahararriyar jarumar finafinan Hausa ta Kannywood Maryam Booth ta dauki wani sabon hoto wanda ta yi domin nuna goyon baya da kuma tunawa da sojojin kasar nan wadanda suke gumurzu domin kare kasar nan a fagen fama a sassa daban daban na kasar nan.


Jarumar mai shekaru 25 da haihuwa ta saka hoton ne a shafin ta na sada zumunta na Instagram, inda ta saka hoton nata sanye da kakin sojojin rike da hular akan cinyarta.

Sannan tayi gajeren rubutu kamar haka “Domin tunawa da sojojin da suke gwagwarmaya domin kare mu da kuma kasarmu baki daya, Allah ka albarki sojojin Najeriya”.

Bayyana wannan sako nata dai ana ganin zai karawa sojin kasar nan kaimi da kwaringwuiwa musamman bayan rahotannin da suka gabata na cewar sojoji 23 sun bace a sakamakon harin yan tada kayar baya na Boko Haram suka kai musu.
https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.