Masarautar Kano Na Kusa da Kafa Doka Kan Yawan Mutuwar Aure

Malam Muhammdu Sunusi Na 2

0 277

 

Masarautar Jihar Kano Na Kusa Da Fitar Da Dokar Kan Yawan Mutuwar Aure

Masarautar Jihar Kano na wani aiki tukuru kan wani kudirin doka, da za ta magance matsalar yawaitar mutuwar Aure, tare da tilasta wa magidanta daukan cikakkiyar dawainiyar iyalansu ta yau da kullum.

Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sunusi na II, ya bayyana hakan ne a yayin ganawarsa da manema labarai a wajen wani taro da Asusun Tallafawa al’umma na Majalisar Dinkin Duniya ya shirya a Birnin Tarayya Abuja.

Alhaji Muhammadu Sanusi na II, da Talban Kano ya wakilce shi, ya ce “Masarautar ba za ta lamunce wa mazaje sakin matansu ba tare da daukan hidimar kulawa da yaransu ba.”

Nan ba da jimawa ba kwamitin da ke aiki kan kudirin dokar, zai kammala aikinsa kafin daga bisani ya gabatar da shi ga Majalisar Dokokin Jihar ta Kano, domin amincewa da shi a matsayin doka.

Cikin kunshin Kwamitin sun hada da manyan alkalan Jihar da Malaman Addinin Mulumci da kuma Malaman ilimin zamani wato na boko.

#Mikiya

Leave A Reply

Your email address will not be published.