Mataimakain Shugaban Kasa a Garin Daura, Ya Ziyarci ‘yar Uwar Shugaba Muhammadu Buharai

0 192

Mataimakain Shugaban Kasa a Garin Daura, Ya Ziyarci ‘yar Uwar Shugaba Muhammadu Buharai.
Shugaban kasa mai rikon kwarya Farfesa Yemi Osinbajo ya ziyarci jihar Katsina ya kuma yadda zango gidan yar uwar shugaba Muhammadu Buhari dake Daura
.
.
Mukaddashin shugaban kasan ya ziyarci Daura ne domin mara ma dan takarar kujerar majalisar dattawa daga yankin baya kana ya ziyarci gidan Hajiya Rakiya Adamuto wanda take ‘ya ga shugaban kasa
.
.
Osinbajo ya halarci taron yakin neman zaben honourable Ahmed Babba-kaita wanda ke takarar sanata karkashin jam’iyar APC a zaben cike gurbi da za’a gudanar ranar asabar 11 ga watan Agusta
.
.
Taron ya samu halartar gwamna Aminu Bello Masari da takwaransa na jihar Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje tare da shugaban jam’iyar APC na kasa Adams Oshiomole
.
.
Sakataren gwamnatin kasa Boss Mustapha da ministan sufurin jirgin sama Hadi Sirika tare da sauran manyan jami’an gwamnati sun halarci taron
.
.
Ahmed Babba-kaita zai fafata da sauran yan takara dake neman maye gurbin kujerar marigayi Sanata Mustapha Bukar wanda ya rasu cikin watan Afrilu. Cikin yan takarar akwai dan uwansa wanda zai fito takara karkashin jam’iyar PDP.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.