Matan Gwamnonin Arewacin Nijeriya Sun Dauki Ɗamara Taimawaka Mawakan Kannywood

0 351

Matan Gwamnonin Arewacin kasar nan hudu da suka hada da matar Gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya Zainab Bagudu da matar Gwamnan Jihar Bauchi, Hajiya A’isha Muhammad Abubakar da matar Gwamnan Jihar Kogi, Misis Rashida Bello da kuma matar Gwamnan Jihar Kaduna, Hajiya A’isha Ummi El-Rufa’i sun yi alkawarin taimaka wa mawakan Arewacin kasar nan musamman na masana’antar fina-finan Hausa da ake kira Kannywood.

Matan gwamnonin sun bayyana kudirinsu na taimaka wa mawakan ne yayin taron kalankuwa da kadammar da albam mai suna ‘Lobe’ da fitaccen mawaki Ali Isa (Jita) ya shirya a dakin taron na Lagos Hall da ke otal din Transcorp Hilton da ke Abuja a ranar Asabar da ta gabata.

Matan gwamnonin sun bayyana niyyarsu ta taimaka wa mawakan Arewa ne saboda irin gudunmawar da suke bayarwa wajen ilimantarwa da fadakarwa da wa’azantawa da kuma nishadantar da al’umma.
A lokacin da Hajiya Zainab Bagudu take jawabi a wurin taron, ta ce ofishinta zai taimaka wa mawakan Arewa musamman na Kannywood don ganin sun bunkasa sana’arsu ta waka.

Ta bayyana cewa mawaka suna da basira da kuma hazaka, kuma suna bayar da gudunmawa sosai kamar yadda likitoci suke ba da gudunmawa a duniya, “Don haka ina sauraren wakoki kuma a cikin mawaka Ali Jita ne gwanina, don haka na sayi albam din ‘Lobe’ a kan Naira miliyan biyar.”

Ta kuma yi alkawarin za ta taimaka wa mawaka sakamakon gudunmawar da suke ba al’umma ta hanyar wakokinsu.
A lokacin da take jawabi, matar Gwamnan Jihar Bauchi, Hajiya A’isha Muhammad Abubakar ta yi alwashin taimaka mawaka ta hanyar ofishinta don ganin mawakan Arewacin kasar nan sun tsaya da kafafunsu.

“Ba zan fadi kudin da zan bayar a wurin wannan kaddamarwar ba, Ali Jita dan gida ne, abin da zan ce shi ne, sai ka zo Bauchi kawai,” inji ta.
Matar Gwamnan Jihar Kaduna, Hajiya A’isha Ummi El-Rufa’i ta kara nanata alkawarinta na taimaka wa mawakan Kannywood.

Ta ce, “Saboda yanayi na siyasa da ake ciki, idan na ambaci kudin da zan sayi albam din zai iya sa a mayar da abin siyasa duk da kyakkyawar manufata ta taimaka wa harkar waka a Arewacin kasar nan. Amma zan ba ka gudunmawa sai dai ba zan fadi ko nawa ba ne.”
Ita ma matar Gwamnan Jihar Kogi, Misis Rashida Bello ta ce za ta taimaka wa mawaka ta ofishinta inda za su yi amfani da wakokinsu wajen yaki da Cutar Sankara.

Leave A Reply

Your email address will not be published.