Mawaki ClassiQ Ya Na Shirye-Shiryen Saka Gasa Mai Taken “New North”

0 185

Up North Recordz suna farin ciki sanar da ku sabon gasar da classik zai saka wanda ba’a taba yin irinsa arewa ba, mai taken “New North”.
Gasar New North din ana shirin gabatar da shi ne a harabar jami’o’in dake Arewa cikin wannan watan da muke Nuwamba.

Gasar tana cike da tarin abubuwan kayatarwa kamar wasannin barkwanci kyaututtuka ga wandanda allah yaba ma sa’a zasu ci.
Daga cikin manyan mawakan da aka gayyata ya hada da irinsu Jesse Jagz, Ruby Gyang, CKay, Kheengz, Lyrical Dr Smith, BOC Madaki, da dai sauransu.
Jadawalin farko na garuruwan da za’a gabatar da wasan ya hada da Plateau ranar 6th ga watan Nuwanba da 8th, Nasarawa 10th ga wata, Abuja 13th ga wata, Kano 15th ga wata, Borno 17th ga wata, sai Adamawa 20th da 21st ga wata.
Ka’idojin shiga Gasar:
Ga masu sha’awar shiga gasar zaku iya sauke App din ALAT a google play ko a Apple Store. Bayan ka sauke sai kayi Rijista.
Kana da damar da zaka iya cin kyauta har na 10,000 in kasa 1000 kacal a cikin a asusunka na ALAT din.
Dan haka mai kake jira? Hanzarta ka sauke App din dan kasancewa tare da gwarzon mawakin Arewa, Classik mai taken AREWA MAFIA.

Leave A Reply

Your email address will not be published.