Mawallafin Jaridar RARIYA, Dakta Aliyu Modibbo Ya Fara Nazari A Jami’ar Oxford Dake Kasar Ingila

0 257

Daga Mahmud Isa Yola

Tsohon ministan birnin tarayya (FCT) kuma mawallafin jaridar nan ta RARIYA Dakta Aliyu Modibbo (Danburan Gombe) zai kasance a shahararriyar jami’ar nan ta Turai ‘Oxford University’ daga watan Janairu da muke ciki.

Dakta Modibbo wanda ya kammala karatun digirin digir-digir shekaru 27 da suka gabata a jami’ar California dake Los Angeles bayan dawowan sa Nijeriya ya karantar a jami’ar Abuja. Daga bisani ya yi aiki da fadar shugaban kasa na tsawon shekaru goma inda ya rike mukamin minista har sau uku.

Aikin nasa a jami’ar Oxford zai kunshi nazari na musamman da zai gudanar tare da gabatar da takaddu a fannonin ilimi guda uku.

Zai yi aiki tare da manyan malaman jami’ar da suka hada da Farfesa Wale Adebanyi, Daraktan cibiyar ilimi ta Afirka a jami’ar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.