Meye Gaskiyar Tallafin N10,000 Na Eyowo??

0 922

Meye Gaskiyar Tallafin N10,000 Na Eyowo??

Menene Tsarin Eyowo?
Tsari ne da zai baka damar karba ko tura kudi ko kuma biyan bills amman ta hanyar amfani da layin wayarka.
Damar sarrafa kudi ba tare da account din banki ba, sannan ba tare da kana da network ba (Data).

Menene Gaskiyar Bada Tallafin N10,000?
Ko kadan tsarin Eyowo baya bada wani tallafi na Naira 10k sannan bashi da alaka da tallafin da shugaban kasa ke bayarwa.

Yaya Akayi Ake Samun 10k A Eyowo?
Abinda bincikena ya tabbatar min shine:
Eyowo: suna yin adashi ne na N50 kamar yadda duk wanda ya nemi kudin zasu zari N50 a layinsa, to idan suka tara mutum 200 kaga 10k sai su turawa mutum daya.
Da zarar mutum daya ya samu sai ya sanarwa ‘yan uwan sa, suma sai su hanzarta sai kaga mutane da yawa sun yi amman kadan ne suke samu.

Kuma ana cikin yin wannan tsarin yanzu haka Eyowo sun fara zarewa masu yi kudade yau din nan naga wanda aka zarewa 70k hakan ne ma ya sanya ni yin wannan rubutun.

Kwadayi Mabudin Wahala!

Basheer Sharfadi
CEO Sharfadi.com
Call & WhatsApp: 09035830253
#BasheerSharfadi #Eyowo

Leave A Reply

Your email address will not be published.