Ministar Kudin Nijeriya Tayi Murabus -Kemi Adeosun

Kemi Adeosun

0 255

Ministar kudin Najeriya, Kemi Adeosun, ta ajiye aikinta kan zargin da aka yi mata na aiki da takardar shaidar dauke yi wa kasa hidima ta boge. Dokar yi wa kasa hidima dai ta Najeriya ta wajabta wa duk wanda ya kammala karatun digiri yana mai kasa da shekara 30 ya yi shekara daya yana yi wa kasa hidima. Hakazalika dokar ta ce wanda ya dara shekara 30, za a ba shi takardar shaidar dauke masa yi wa kasa hidimar.
A wasikar ajiye aiki da ta rubuta ga Shugaba Buhari, kuma ta wallafa a shafinta na Twitter, Adeosun ta ce ta kasance tana zama a Birtaniya a matsayin ‘yar kasar har ta kai shekara 34. Wannan ne ya sa da ta dawo Najeriya aka yi ta tattaunawa kan ko dokar ta yi wa kasa hidima ta shafe ta a lokacin ko kuma a’a.
Daga nan kuma aka ba ta shawarar karbar takardar shaidar dauke yi wa kasa hidima. Ta kara da cewa wannan ne ya sa ta nemi abokan huldarta su karba mata.
Ta ce tun da dai ba ta taba zuwa ofishin hukumar NYSC ta yi wa kasa hidima ba, ba ta da hujjar tunanin cewar takardar da aka ba ta ta boge ce. #KemiAdeosun #Nigeria #NYSC

Leave A Reply

Your email address will not be published.