Na Tafi Hutun Fitowa A Fina-Finai, Shin Ko Mene Dalili?

0 270

A yamma cin ranar Jama’a ne Jarumi Adam A Zango ya bayyana cewa zai tafi hutun fitowa a fina-finai har na tsawon wata uku.

Jarumin dai yace yana fata baza’a canja masa magana ba inda yace zai dawo fitowa acikin watan April na 2019 ko me yasa Jarumin daukar wannan matakin?

Zamu iya cewa kowa yakwana ya tashi yasan Zango yana daya daga cikin mutanen da suke yawan samun sabani da abokan aikin sa Inda yake musu lakabi da masu yi masa hassada.

Duk dai bai bayyana taka mai-mai dalilin da yasa zai tafi wannan hutu ba amma wasu suna zargin baya rasa nasaba da sabani da abokan aikinsa ko kuma yana so ya huta na wani lokaci.

Leave A Reply

Your email address will not be published.