Nafisa Abdullahi – Abin Da Yasa Na Daina Soyayya Da Adam A Zango

0 178

Shahararriyar jarumar fina-finan Hausa na Kannywood Nafisa Abdullahi ta bayyana cewa sun dauki tsawon lokaci ba sa tare da abokin sana’arta jarumi Adam A. Zango.

Jarumar ta bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da BBC, inda ta kara da cewa dama Allah ne ya hada su kuma yanzu ya raba su.

“Kusan shekaru hudu ke nan ko biyar ba ma tare, kamar yadda Allah ya hada haka kuma yanzu ya raba. Zama ne kawai ya zo karshe,” in ji ta.

Har ila yau an tambaye ta ko yaya yanayin alaka yake yanzu a tsakaninta da shi.

Sai ta ce alakarta da shi ba soyayya ba ce, abokin aikinta ne kawai. Idan ba su hadu a wani wuri ba, to za su hadu a wani duk da cewa sun fi yin aiki tare a baya kuma an fi ganinsu tare.

A baya dai an sha zargin alakar soyayya tsakanin Nafisa da Adam Zango inda aka sha ganinsu tare a bainar jama’a da kuma fina-finai masu yawa da suka taka rawa tare a matsayin jarumai.

BBC hausa

Leave A Reply

Your email address will not be published.