Najeriya: An haramta zuwa zabe da wayar salula

zaben Nijeriya

0 264

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta haramta zuwa wurin kada kuri’a da wayar salula.

Mai magana da yawun hukumar, Malam Aliyu Bello – wanda ya tabbatar wa BBC da wannan labari – ya kara da cewa sun dauki matakin ne domin magance matsalar magudin zabe.

A cewarsa, za su soma tabbatar da haramcin ne a zaben da za a yi a jihar Osun da ke kudu maso yammacin kasar ranar Asabar mai zuwa.

“Yin haka na daga cikin matakai da hukumar zabe ta dauka domin ta rage barna da ake tafkawa a daidai lokacin da ake kada kuri’a… hukumar na kokarin gano dabaru da salon yadda za a gudanar da zabe nagartacce ne,” in ji shi.

Malam Aliyu ya ce bisa fahimtarsu, masu sayar da kuri’unsu suna kulla yarjejeniya ta yadda masu sayar da kuri’a za su nuna wa masu saye wata shaida da za ta gamsar da su cewa jam’iyyarsu mutum ya zaba gabanin su biya shi, don haka wannan dokar za ta magance wannan matsalar.

Jami’in na hukumar zabe ya yi kira ga ‘yan kasar su ba su hadin kai wurin ganin sun aiwatar da dokar ba tare da fuskantar matsaloli ba.

Ana zargin ‘yan siyasar Najeriya da yin mfani da kudi wurin sayen katin zabe da ma kuri’u a yunkurin da suke yi na yin magudin zabe, ko da yake sun sha musanta zargin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.