Najeriya Na Daf Da Shiga Matsalar Wutar Lantarki Ta Kasa Baki Daya – GENCoc

0 136

Najeriya Na Daf Da Shiga Matsalar Wutar Lantarki Ta Kasa Baki Daya – GENCoc.
Kamfanonin da ke samarwa da raba wutar lantarki, GENCos, sun yi kakkausan gargadin cewa Najeriya na daf da afkawa cikin matsananciyar wahala da kuma matsalar wutar lantarki.

Babbar Sakatariyar Kungiyar Kamfanonin Samar da Hasken Lantarki, APGC, Joy Ogaji, shi ne ya yi wannan gargadin yau Alhamis, cikin wata takardar sanarwar da ta tura wa PREMIUM TIMES a yau da yamma.

Ogaji ta ce gaba dayan injinan samar da wutar su na ta haska danjojin da ke nuna cewa a kowane lokaci za su iya tsayawa,su daina aiki.

Bai ta dai ce ga rana ko lokacin da injinan za su tsaya ba, sai dai kawai ta yi jawabi tamkar gargadin kwana da shiri, inda ta ke cewa, “Za su iya tsayawa a gobe, ko yau ko nan da wata daya, ko ma wane lokaci. Na yi magana ne tun yanzu domin a san halin da ake ciki, kada sai bayan sun tsaya, kasa ta fada cikin duhu ‘yan kasuwa su ce laifin GENCos ne.”

Ta ce dalilin da injinan za su iya tsayawa cak, shi ne saboda Kamfanin Raba Wuta na Najeriya, TCN, ya kasa jan wutar da ya kamata ya kwasa ya kai cikin tashar tattara hasken lankarki ta kasa, National grid.

Misalin da ta bayar shi ne, cikin watan Afrilu an samu karfin wuta har migawat 7,485, amma TCN ta iya zukar migawats 3985 ta raba wa GENCos kawai.

Ogoji ta ce duk da ana ta murnar Najeriya na samun migawats 7,500 a yanzu, cibiyar tattara hasken wutar lantarki ta kasa, ba ta iya kwasar sama da migawats 4,500.

Su kuma masu aiki da sayar da hasken lantarki, sun ce karfin wutar lantarki fiye da migawats 5000 a Najeriya, zai ki karbuwa a hannun DISCOs da TCN, saboda babu isasshen matattarar karfin lantarki da kuma wuraren karkasa shi, hususan saboda matsaloli irin su yawan tsinkewar layuka, yawan lalacewar tiransifomomi da kuma karfin maganadison wutar lantarki.

A karshe Ogoji ta ce abin kamar kayan da ake amfani da lantarki da su ne, irin su firji, radiyo da talbijin da sauran su. Wadanda ta ce idan wuta ta yi musu kadan, ba za su iya aiki ba. Idan kuma ta yi musu yawa, su lalace

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.