Nasha Wahala Leceister City, Cewar Ahmed Musa

Leceister City Ahmed Musa

0 254

Kan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr dake kasar Saudiyya wanda yayi zaman aro a kungiyar CSKA Moscow, Ahmad Musa, ya bayyana cewa tsohuwar kungiyar ta sa ta Leceister City bata bashi wata dama ba da zai nuna kansa tun bayan da aka samu canjin mai koyarwa a kungiyar.

Ahmad Musa, wanda ya zurawa tawagar ‘yan wasan Super Eagles ta Najeria kwallayenta guda biyu da suka bata damar doke kasar Iceland daci 2-0 a wasa na biyu na gasar cin kofin duniya ya bayyana cewa tun lokacin da kungiyar ta sake sabon mai koyarwa ya daina buga wasa.

“Lokacin da nakoma kungiyar ina buga wasa amma bayan an kori Claudio Ranieri sai aka mayar dani benci aka daina yin amfani dani sosai kuma babu wanda ya gayamin dalilin hakan amma kuma nasha wahala” in ji Ahmad.

Ya kara da cewa “ Sai da nayi watanni bakwai ina zaman benchi kafin kuma tsohuwar kungiya ta taga bai kamata inyi zaman benchi ba kuma suka ce suna bukata ta a matsayin aro ni kuma na amince saboda daman gidana ne”

Ahmad, wanda tsohon kan wasan kungiyar BBB Benlo ne ya bugawa Leceister City wasanni 33 a lokacin Ranieri da kuma bayan an koreshi sai dai kawo yanzu yana buga wasanni a sabuwar kungiyarsa ta Al-Nassr ta kasar Saudiyya.

Ahmad Musa shine kan wasan Najeriya na farko a tarihi daya zura kwallaye huku a gasar cin kofin duniya bayan ya zura a wasan Najeriya da Argentina a gasar cin kofin duniya na shekara ta 2014 wanda akayi a kasar Brazil sai kuma kwallayen daya jefa a ragar kasar Iceland a wannan shekarar da aka buga a kasar Rasha.

#HausaleaderShip

Leave A Reply

Your email address will not be published.