Ni ne nafi dacewa in zama dan takarar shugaban kasa a PDP, Inji Makarfi

0 193

Ni ne nafi dacewa in zama dan takarar shugaban kasa a PDP, Inji Makarfi.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Sanata Ahmed Makarfi ya bayyana cewa shine yafi dacewa ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa.


Makarfi ya bayyana haka ne a ci gaba da ganawa da wakilan jam’iyyar PDP da yake yi, wannan karon a garin Ado- Ekiti.
Makarfi ya ce shi gogagge ne a harkar gudanar da mulki, da hakan ya sa ya kware a harkar iya jagorancin mutane.
” Ku duba yadda na yi mulki a jihar Kaduna. Na tabbata na hada kan mutanen jihar, na yi abin da ba a taba yi ba a jihar na ci gaba wato raya karkara da birane.
” Sannan a lokacin da jam’iyyar mu ta PDP ta fada cikin rudani, a matsayin shugaban jam’iyyar na riko na tabbata an samu daidaituwa cikin kwanciyar hankali sannan an saita jam’iyyar ta dawo kan hanyar da ta dace.
” Matsalolin da na iske a lokacin da na zama gwamnan Kaduna basu misaltuwa, bayan talauci da mutane ke fama da shi a wancan lokaci, makarantun mu sun lalace, sannan kuma kabilanci da rabuwa na addini yayi wa mutanen jihar katutu.
” Duk sai da na tabbata anyi abin da ya kamata kafin wa’adin mulkina ya cika.
Bayan haka Makarfi ya soki jam’iyyar APC game da kira da ta ke yi na a tsige shugaban majalisa Bukola Saraki wai don ya canza sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP.
” Ai APC ba ta da yawan da za ta iya tsige shugaban majalisa. Dole sai an sami akalla kashi biyu bisa uku na sanatoci kafin a iya tsige shugaban Majalisa. Kuma basu da shi.
Game da takawar da Buhari yayi kuwa ranar Sallah Makarfi ya ce, ba sai an tallata cewa Buhari ya yi tattakin mita 800 ba kafin a sani ko yana da lafiya ko baya da shi ba.
” Motsa jiki abu ne da nike yi kullum a rayuwa ta ba sai na tallata haka ba. ”
Idan ba a manta ba Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wasu baki da suka ziyarce sa a Daura cewa ya taka da ga masallacin Idi zuwa gida ne domin ya gaggaisa da mutanen sa.
” Ni ban taka daga masallacin Idi zuwa gida don in burge kowa ba. Tun bayan da na fito daga masallaci sai naga dandazon jama’a suna ta miko gaisuwa.
” Da na ga haka sai na fito domin in yi amfani da wannan dama mu gaggaisa da jama’a. Da yawa cikin su na son su ganni amma basu sami wannan dama ba. Wannan shine babban dalilin da ya sa na fito na taka zuwa gida.” Inji Buhari.
Makarfi ya ce lallai shine ya fi zama dantakarar da ya fi dacewa wakilan jam’iyyar su zaba domin fafatawa da Buhari a 2019.
Premiumtimeshausa.
https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.