Nigeria zata Gina Layin Dogo Wanda zai taho Daga Fatakwal Zuwa Jamhuriyar Nijar

0 114
Nigeria tana Shirye-Shiryen Gina Layin Dogo Wanda zai taho Daga Fatakwal Zuwa Jamhuriyar Nijar.

Nigeria tana Shirye-Shiryen Gina Layin Dogo Wanda zai taho Daga Fatakwal Zuwa Jamhuriyar Nijar

Nigeria  tana Shirye-shiryen gina layin dogo wanda zai taso daga Fatakwal ya ratso wasu jahohin Najeriya kana ya wuce jamhuriyar Nijar, domin inganta rayuwar al’umma da muamala da juna.

Majalissar Ministocin Najeriya ta amince da mahimman abubuwa guda uku da zasu ciyar da kasar nan gaba tare da inganta rayuwar al’ummarta.

Wadannan muhimman abubuwa sun hada da kiwon lafiya da sufuri da kuma alamuran da suka shafi bulaguro tsakanin kasa da kasa.

Majalisar ta bada amincewarta akan bukatar dake akwai na gina layin dogo tsakanin Fatakwal da Abuja da Kaduna da Katsina da Kano da Maiduguri sannan ya wuce zuwa jamhuriyar Nijar. Wannan na cikin yunkurin da gwamnati ke yi na bunkasa harkokin kasuwanci da cinikayya tare da inganta muamalar al’umma.

Baicin gina layin dogo majalisar ta amince da daukan matakai akan sha da shigowa da sigari cikin kasar. Kazalika za’a inganta ayyukan jami’an shige da fice na kasar ta tattara bayanan sirri da bayanai akan masu shiga da fita Najeriya.

Ministan kula da harkokin cikin gidan Najeriya Janar Abdulrahaman Dambazzau ya ce za’a gina wa hukumar shige da fice babban gini da zai kunshi duk kayayyakin aikin da suke bukata, ta hakan za’a tattara duk bayanan masu shigowa da fita.

Akan layin dogon da za’a gina tsohon shugaban sufuri ta Najeriya Malam Suleiman Dan Zaki ya yaba da yunkurin gina layin dogon saboda mahimmancinsa wajen inganta cinikayya da muamalar ‘yan kasa. A cewarsa layin dogo zai rage yawan anfani da titunan moto wajen daukan kaya da mutane.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.