PDP Ta Bani Cin Hancin Makudan Miliyoyi Don Na Bar APC – Sanata Binta

0 176

PDP ta bani cin hancin makudan miliyoyi don na bar APC – Sanata Binta

Sanata Binta Garba mai wakiltar Adamawa ta Arewa ta ce jam’iyyar PDP ta bata cin hancin kudi sama da N300,000,000 domin ta fice daga jam’iyyar APC ta koma PDP amma ta ki amincewa ta bukatarsu.

Sanata Garba ta yi wannnan furucin ne a wajen yakin neman zaben ta a Yola gabanin gudanar da zaben fidda gwani a jihar, ta ce PDP ta yi mata alkawarin kudin ne domin ta taimaka wajen rage kuri’un gwamna Mohammed Bindow.

Sai dai daga baya gwamna Bindow da jam’iyyar APC sun lashe zaben gwamna a jihar tare da kujerun sanata uku a shekarar 2015.

Sanata Garba ta ce rashin amincewa da tayin da jam’iyyar PDP ta yi mata ne ya kiyaye afkuwar rikici a jam’iyyar ta APC reshen jihar Adamawa.

Sanatan ta na neman takara domin sake komawa majalisar ta dattawa sai dai a halin yanzu akwai wasu ‘yan takara maza uku da ke neman fafatawa da ita.

‘Yan takarar sun hada da Mai bawa tsohon shugaban Jonathan shawara kan harkokin siyasa, Mamman Tahir, Tsohon shugaban makarantar horas da lauyoyi kuma Ciyaman din Hukumar Lafiya bai daya, Abdullahi Belel, da Dan majalisar wakilai na tarayya mai wakilatar Michika da Madagali Adamu Kamale.

#Mikiya

Leave A Reply

Your email address will not be published.