Pogba Ya Amince Da Komawa Barcelona

Pogba - Barcelona

0 246

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Paul Pogba, ya amince da komawa kungiyar Barcelona dake kasar Sipaniya kamar yadda rahotanni suka bayyana daga kasar Faransa.

Dangantaka dai tayi tsami tsakanin dan wasa Paul Pogba da kociyan kungiyar Jose Mourinho, wanda takai har Mourinho din ya kwace mukamin mataimakin kaftin daga hannun dan wasan.

Tuni dai aka bayyana cewa Pogba ya kammala shirinsa na komawa Barcelona daga United a kakar wasa mai zuwa idan har abubuwa basu canja ba a kungiyar nan da wasu ‘yan lokuta.
Mai kula da harkokin wasannin dan wasan, wato Eja, Minio Riaola, tuni aka bayyana cewa ya amince da ciniki da Barcelona kuma zaiyi kokarin ganin yakai dan wasan kasar ta Sipaniya.
Sai dai kuma shugabannin kungiyar Manchester United basa son rabuwa da dan wasan wanda suka siyo daga Jubentus akan kudi fam miliyan 89 a shekara ta 2016 kuma a shekarar yafi kowanne dan wasa tsada a duniya.

Pogba dai yana ganin Mourinho baya amfani dashi yadda yakamata kuma abubuwa da dam sun hada dan wasan da Mourinho wanda akayi rade radin cewa za’a koreshi a kwanakin baya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.