Queen Zeeshaq Tayi Abin Mamaki Daba Ai Zato Zatayi ba

0 1,512

Fitacciyar Mawakiyar HipHop kuma ma’aikaciyar Gidan Radio “Vision FM” Wacce ke gabatar Da Shirin “Hip-Hop Square” Wato “Zainab Ishaq” wacce akafi sani Da “Queen Zeeshaq” Yar Asalin Jihar Kano, Tayi abinda Ba’a taba Samun wata Mawakiya Mace datai ba.

Shirin “Hausa Hip-Hop Square” da Wannan Fitacciyar Mawakiya ke Gabatarwa A Gidan Radio “Vision FM” ya Samu Karbu a Jihar Kano dama Arewacin Nigeria, Inda A Cikin wannan Shirin Ake Gayyato Mawaka da Duk wani Wanda Yake da alaka da Music Industry.

Queen Zeeshaq tana daya daga Cikin Mawaka mata Wanda akafi sauraro a Arewacin Nigeria, Da wasu sassa Na kasar nan, Fitattatun wakokin da sukafi shahara a Shekarar nan, na ita wannan Mawakiya, akwai irin su “Hajiya Babba, Wata Rayuwa, Ramadan da dai sauran su…

QUEEN ZEESHAQ TAYI ABINDA BA’A TABAYI BA.

A wannan Shekarar da Muke Ciki 2019 cikin watan Jun, ne wannan Fitacciyar Mawakiya Ta Samu Lambar Yabo (Award) Har Guda Uku (3) cikin Kwanaki Uku (3) A Jere…

Lambar Yabo (Award) Ta Farko (1): Ta Fito ne Daga Masoya Shirin Wannan Mawakiya wato (Hausa Hip-Hop Square Fans Club) Inda Wannan Masoya Nata Suka duba Irin Cancanta Da kuma jajircewa Da Baiwa, Da Allah (S.W.A) ya Baiwa wannan baiwar Allah.

Inda Washe Gari Kuma aka sake Bata Wata Lambar Yabon (Award) 

Lambar Yabo (Award) Ta Biyu (2): Ta Fito ne Daga Hannun Wani Group, Wato (Yan Arewa Group Chart) Inda Suka Duba Cancanta, A Matsayin Ta Na Mawakiyar Hip-Hop Mace suka Karramata (Best Female Hausa Rapper).

 Washe Gashi, Karramawa Ta Uku (3) 

Lambar Yabo (Award) Ta Uku (3): Ta Fito ne Daga Hannun Wani Kungiya (New Mai Tashe) Inda Nan Ma Suka karramata Da Lambar Yabo…

Fatan Nasara gare ki Da Daukaka Na Har Abada  (Mr ArewaRulers)

For Music Or Video Promoting Contact Us, Call/WhatsApp: 08161892123 or Email: Support@arewarulers.com

Leave A Reply

Your email address will not be published.