Rahama Sadau Ta Sake Samun Lambar Yabo Ta Best Actress Of Year 2018 Na “Peace Builder 2018”
Rahama Sadau
Har yanzu tauraron fitacciyar jaruma Rahama Sadau na cigaba da haskawa inda Ta samu wani sabon lambar yabo a karshen makon da ya shude.
Jarumar ta samu kyautar jaruma mai bada taimako wajen haddasa zaman lafiya a bikin Peace Achievers Awards 2018 wanda aka gudanar ranar Asabar 22 ga watan Satumba a dakin taro na Transcorp hilton Hotel dake Abuja.