Rahama Sadau tace ita ba zata shiga gasar saka tsaffin hotuna da ake yi ba

0 323

A yayin da ake tsaka da gasar saka hotunan da aka dauka shekaru goma da suka gabata a shafukan sada zumunta, musamman tsakanin taurarin fina-finai ko mawaka, tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta ce ita ba za ta yi wannan abu ba.

Rahamar ta bayyana hakane a shafinta na dandalin Twitter inda ta rubuta cewa, Tab gaskiya ni ba zan yi wannan 10 years challenge din ba.
Shahararren me bayar da umarni Hassan Giggs ya ce mata, Rahama Sadau muna so muga hotonki, amma sai ta bashi amsar cewa, bani da shi gaskiya.


Leave A Reply

Your email address will not be published.