Rahama Sadau tayi Murnar cika shekaru 25: Kalli zafafan hotunan da suka rikita maza

0 2,222

Shahararriyar jarumar shirya fina finan Hausa, Rahama Sadau, wacce tayi fice da sunan Halwa, tun bayan da ta dauki wani shiri mai taken “Halwa”, ta yi bukin murnar zagayowar ranar haihuwarta, cikin salon da ya dauki hankali jama’a, musamman ma maza daga masoyanta.

A ranar 6 ga watan Disamba, jaruma Rahama Sadau, wacce tuni tauraruwarta ta ke haskawa a bangaren shirya fina finan kudancin Nigeria, ta cika shekaru 25 a doron duniya. Rahama Sadau, ta wallafa wasu zafafan hotunanta a shafukanta na yanar gizo, da suka hada da Twitter da Instagram, ta godewa Allah da ya bata tsawon ran sake ganin wannan rana, tare da gode masa akan dukkanin ni’imomin da ya yi mata.

Jarumar tace: “Na godewa Allah da na samu tsawon kwana har zuwa wata sabuwar shekarar a rayuwata. Godiya ga Allah da na sake ganin wata shekarar cike da dariya, soyayya da kuma ganin abubuwan ban mamaki. Na godewa Allah da wannan kyakkyawar rayuwa mai daraja da ya bani.” Legit.ng Hausa, ta tattara rahoto kan cewa, daga cikin wadanda suka taya jarumar murnar zagayowar ranar haihuwarta, akwai mai tallafawa shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fuskar kafofin sadarwa na yanar gizo, Bashir Ahmed, tare da jarumi Ali Nuhu, Adam A Zango, Nuhu Abdullahi, da dai sauran abokanan sana’arta dama furodusoshi kamasu Bashir Maishadda, da kuma daraktoci irinsu Aminu S Bono da dai sauransu.

Kalli Zafafafan hotunan da ta dauka:-

Leave A Reply

Your email address will not be published.