Ronaldo na Gab Da Tafka Mummunar Asara

Ronaldo

0 269

Kamfanin da ke yin kayan wasanni na duniya (Nike) dake Amurka, da ya shahara wajen sana’anta kayayyakin wasanni ya ce, ya damu matuka, dangane da zargin cin zarafi ta hanyar aikata fyade, da ake yiwa dan wasan Juventus Cristiano Ronaldo.

Nike, wanda ya kulla yarjejeniyar dala biliyan 1 da Ronaldo ta ban gishiri in baka manda, ya ce zai ci gaba da bibiyar yadda lamarin zargin da ake yiwa dan wasan ke warwara, domin tantance makomar yarjejeniyar da ke tsakaninsu.

A gefe guda, kamfanin EA Sports da shima ya shahara wajen sana’anta na’urorin wasannin bidiyo musamman na kwallon kafa, wanda shi ma ke da yarjejeniya da Ronaldo, ya ce ya soma nazarin makomar alakar da ke tsakaninsu.

Tun a ranar Larabar da ta gabata, Cristiano Ronaldo ya sake musanta zargin da Kathryn Mayorga ta yi masa, na cin zarafinta ta hanyar fyade, a wani Otal din Las Vegas dake Amurka a shekarar 2009.

Akwai fargabar cewa lamarin ka’iya shafar yarjejeniyoyin da Ronaldo ya kulla da kamfanonin, abinda ka ‘iya haifar masa da nakasu wajen makudan kudaden da yake samu.
Sai dai kungiyar dan wasan wato Juventus ta cezargin da Kathryn Mayorga ke yiwa dan wasanta Cristiano Ronaldo ba zai shafi kyakkyawar alakar dake tsakaninsu ba.

Juventus ta ce ta gamsu da irin gudunmawar sabon dan wasan nata, da kuma irin kishin da yake nunawa ci gabanta, dan haka shugabanni da magoya bayanta suna bayan Ronaldo.

Leave A Reply

Your email address will not be published.